Labaran Hausa

Rundunar Yan Sandan Jahar Ogun Tasamu Nasarar Kama Wani Matashi dayayiwa Wani Yaro Fyade Yanzu…

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya ta sanar da cewa ta kama wani matashi da take zarginsa da yi wa wani karamin yaro mai shekara biyar fyade, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar yaron.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta ogun Abimbola Oyeyemi ya sanya wa hannu ya ce an kama matashin ne mai shekaru 36 bayan da shugaban kungiyar ci gaban al’umar yankin ya kai korafin matashi zuwa ofishin ‘yan sandan jihar.

Bayan samun rahoton ne sai shugaban hukumar’yan sanda na ofishin ya yi gaggawar tura jami’an tsaron su inda nan take suka kamo wanda ake zargin, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Yayin da ‘yan sandan suka tuhumi wanda ake zargin ya tabbatar wa da jami’an cewa shi mai neman maza shine dalilin da ya sa kenan ya haike wa yaron har rai yayi halinsa”.

Tuni dai kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Ogun ya bayar da umarni kan cewa a mayar da batun sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar domin fafada bincike akan lamarin.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarin Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button