Labaran Hausa

Yanzu-yanzu Gwamnatin Jahar Kano ta Rufe Wani Babban Kamfanin Sarrafa Karafa a…

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wani babban kamfanin sarrafa karafa na yan kasar China bisa karya dokar tsafta da kamfanin yayi.

Kwamitin kula da tsaftar muhalli na jihar ya rufe wani babban kamfanin sarrafa karafa ta kasar China, YoungXing Steel da ke Kano a jiya Asabar bisa karya dokar tsaftar muhalli na wata-wata da kamfanin yayi

Haka kuma ta ci tarar kamfanin kimanin Naira miliyan 5.

Kotun tafi da gidanka ta kwamitin, karkashin jagorancin Alkalin kotun Auwal Sulaiman, ta ba da umarnin a rufe wannan Kamfanin tare da sanya tarar kamfanin YoungXing Steel.

Kazalika, kotun tafi da gidan na ka tanci tara wani gidan mai, MAM Oil and Gas Naira dubu 500 saboda karya dokar ta tsaftace muhalli.

Shugaban kwamitin, Kabiru Getso ya shaidawa manema labarai cewa, kamfanin na kasar China, baya gudanar da aiki a lokacin dokar tsaftar muhalli, ya na kuma keta hakkin ma’aikatan nasa.

“Ma’aikatan kamfanin ba sa saka kayan kariya a yayin da suke gudanar da aiki kuma su na aiki ne da manyan karafa da za su iya illata su koma suyi kisa.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarin Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button