Labaran Duniya

Nasir El-Rufa’i Yace Tsarin Biyan Kudin Makaranta ga Daliban Sakandiri Ya…

Gwamnan jihar Kaduna dake arewacin Nigeria Malam Nasir El-Rufai, ya ce tsarin biyan kudin makaranta ga daliban sakandiren jihar ta kaduna da ma’aikatar ilimin jihar ta bullo da shi ya ci karo da tsare tsaren gwamnatin jihar.

A baya bayan nan dai ma’aikatar ilimin jihar Kaduna ta fitar da sanarwar da take cewa daliban sakandire a jihar za su fara biyan kudin makaranta.

A wata sanarwa kuma da mataimakin gwamnan jihar na musamman kan harkokin yada labarai Muyiwa Adekeye ya sanya wa hannu gwamnan jihar El-Rufa’i ya bayyana tsarin ilimi kyauta a matsayin babban burin da gwamnatin tasa ta sanya a gaba.

Sanarwar ta ce gwamatin jihar Kaduna za ta ci gaba da aiwatar da wannan tsarin ilimi kyauta ga daliban sakandire a fadin jihar.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button