Labaran Hausa

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Tabbatar wa da Yan Nigeria Cewa Bazata iya…

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta kara tabbatar wa ‘yan Nigeria cewa ba za a taba iya yin kutse domin sauya bayanan da ke cikin na’urorin tattara sakamakon zabe ba sakamakon tsaron da aka saka.

Babban mataimakin shugaban hukumar zaben mai lura da sashen fasahar zamani Lawrence Bayode shine ya tabbatar da haka a lokacin da yake amsa wasu tambayoyi a wani shiri na gidan Talbijin din Channels TV .

Yana mai cewa ba za a taba iya yi wa na’urar kutse a ranar zabe ba saboda canza sakamakon zaben.

”Ina so in sake tabbatar wa yan kasa da cewa mun yi duk wani abin da ya kamata domin ganin mun tabbatar da cewa ba a yi wa na’urar kutse ba, za a kiyaye dukkan wasu bayanan da ke cikin na’urar”.

“Bayan kammala zaben, idan za a turo da bayanan zuwa babbar na’urarmu, za a kiyaye dukkan bayanan a lokacin da ake turo su, sannan bayan sun zo babbar na’urarmu,za a ci gaba da lura tare da kiyaye su”,

Sannan ya kara da cewa hukumar zaben ta tsaurara matakai masu tsauri domin ganin ta tabbatar da cewa ba a yi kutse wa na’urorin hukumar ba.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button