Labaran Hausa

Yanzu-yanzu Kungiyar Malaman Jami’a ta Nigeria ASUU Ta Soki Gwannatin Tarayya a…

Kungiyar Malaman jami’a ta Najeriya ASUU ta soki gwamnatin tarayya sakamakon biyan malaman jami’o’in kasar rabin albashin watan Oktoban daya gabata.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar malamn ta ASUU ya fitar a ranar Talata, ya ce kungiyar tasu ta yi Allah wadai da irin biyan da gwamnatin tarayyar ta yi wa mambobinta.

Haka kuma sanarwar daya fitar ta zargi gwamnatin Tarayya da yunkurin mayar da malaman jami’a ma’aikatan wucin-gadi, wadanda za su yi aiki a biya su a nan take ba tare da wani jinkiri ba.

Wannan na zuwa ne dai bayan da gwamnatin tarayya ta biya malaman rabin albashin watan Oktaban daya gabata, tana mai cewa ba za ta biya malaman kudin aikin da ba su yishi ba.

A ranar 14 ga watan Oktoban da ya gabata ne kungiyar ASUU ta janye yajin aikin da ta shafe watanni takwas suna yajin aiki, bayan da kotun ma’aikata ta umarci malaman da su koma bakin aiki.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button