Toffa Yadda Su Asuwaju Bola Ahmad Ke yakin Neman Zaben A…

Darakta-Janar na yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar All Progressive Congress APC, Gwamna Simon Lalong, ya amince da shigar da ‘yan Kannywood cikin kwamitin yakin neman zaben.
Lalong, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Plateau, ya sanar da amincewar tasa a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dr Makut Maham, ya fitar a yau Talata a garin jos dake jihar ta plateau.
Ya ce shigar da yan kannywood wani bangare ne na kokarin zurfafa shigar da masu fasaha daga shiyyar Arewa a yakin neman zaben.
Babban daraktan yakin neman zaben ya ce amincewar ta sa ta biyo bayan ziyarar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ta APC, Sanata Bola Tinubu ya kai jihar Kano, inda ya gana da ‘ya’yan kungiyar.
Ya kara da cewa, Tinubu ya yi alkawarin tabbatar da cewa an baiwa ‘yan Kannywood din damar shiga cikin yakin neman zabe domin su baje kolin basirarsu, tare da taimakawa jam’iyyar ta samu nasara a zabukan dake tafe na shekarar 2023.
Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.