Toffa Babbar Magana, Kungiyar Mata Yan Majalissa Na Shirin Nada Mace Don Kawo Karshen Boko Haram Yanzu…

Ƙungiyar mata yan majalisa ta kasa Najeriya ta yi kira kan cewa a nada mace a matsayin ministar tsaron Nigeria domin shawo kan matsalar tsaron da’ake fama da ita.
Shugabar kwamitin majalisar wakilai kan mata Taiwo Oluga ce ta yi wannan kiran a ranar Litinin a dai dai lokacin taron ganawa da manema labarai a Abuja.
Ta ce “Idan har gwamnati ta nada mace a matsayin ministar tsaron kasar, to kuwa za a ga aiki da cikawa, za ku ga sauyin da za a samu a bangaren tsaron kasar baki daya.”
Kana ta nuna takaicin ta kan yadda kasar Najeriya ta kasance a baya-baya wajen shigar da mata a harkkokin gwamnati.
Ta kara da cewa bayanai na nuna cewa koda ace dukkanin matan da za su tsaya takara a Najeriya za su yi nasara, za a ci gaba da fuskantar matsalar karancin mata a tafiyar da lamurran gwamnati.
Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.