Dan Wasan Kwallon kafa IVory Coast Didier Drogba ya Musanta A…

Tsohon dan wasan kwallon kafar Ivory Coast Didier Drogba ya musanta labaran da su ke ta yawo kan cewa ya musulunta, bayan da wani babban malami ya wallafa hotonsa tare da tsohon dan kwallon kafan suna addu’a a shafinsa na Tuwita.
Malamin ya wallafa hoton nasu ne, tare da cewa tsohon dan kwallon kafan ya musulunta.
To sai dai kuma a wata sanarwa da tsohon dan kwallon kafanbya wallafa a shafinsa na Tuwita, Drogba ya ce ba musulunta ya yi ba, addu’a kawai yake yi wa musulman yankin kauyensu bayan da ya ziyarci kauyen nasu.
Ya bayyana cewa lokaci ne kawai na nuna ”’yan uwantaka”
Daga baya malamin mai suna Mohamed Salah ya goge sakon da ya wallafa din, inda ya bayyana cewa Drogba ba musulunta ya yi ba, to amma kuma zai ci gaba da yi masa addu’ar musulunta idan har Allah yasa yana da rabo.
Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.