Labaran Hausa

DaDuminSa, Wata Babbar Kotun Tarayya Dake Garin Abuja Tasamu Shugaban Hukumar Yakida Cin Hanci a…

Wata babbar kotun tarayya dake garin Abuja, ta samu shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa Najeriya, Abdulrasheed Bawa da laifin saba wa umurnin kotu, a wani hukunci da ta yanke a ahekarar 2018.

A hukuncin da ya yanke yau a Talata, mai shari’a Chizoba Oji ya ce hukumar ta EFCC ta ki aiwatar da wani hukuncin da kotu ta yanke a 21 ga watan Nuwamban shekarar 2018, inda ta umurci hukumar ta EFCC da ta mayar wa wani mutum motarsa kirar Range Rover da kuma kudin sa naira miliyan 40.

Babbar kotun ta bukaci da a tura shugaban hukumar ta EFCC gidan kaso har sai ya wanke kansa daga laifin da ya aikata

Haka nan kuma kotun ta bukaci sifeta janar na yan sandan Najeriya da ya tabbatar an aiwatar da wannan hukuncin da kotu ta yamke akan sa.

Wanda hukuncin na 2018 ya bukaci da a mayar wa mutumin kayan nasa ne ya shigar da kara, inda yake zargin hukumar ta EFCC da kin bin umurnin da kotu ta bayar a hukuncin na farko.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button