Labaran Hausa

Yanzu-yanzu Kungiyar Man Fetur ta IPMAN Tayi Kira ga Tsohon Sarkin Kano a…

Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta IPMAN, ta yi kira ga tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da kuma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i da su daina yin kalaman da basu dace ba a kan harkokin mai da kuma iskar gas.

Kungiyar ta ce, da halin da kasar ke ciki a na tattalin arziki, cire tallafin man fetur baki daya zai kara jawo wa yan kasar wahala, musamman ma talakawan dake kasar.

Kungiyar ta IPMAN ta mayar da martani kan kalaman Sanusi a wajen taron tattalin arziki da zuba jari na Kaduna karo na 7, inda ya ji tausayin shugaban kasa mai jiran gado saboda irin kalubalen tattalin arzikin da ke jiran sa, musamman ma batun tallafin man fetur da kuma biyan basussuka.

Shugaban kungiyar ta IPMAN, reshen Arewacin Nigeria, Alhaji Bashir Dan malam ne ya bayyana hakan yayin da yake zanta wa da wasu manema labarai a jihar Kano a yau Talata.

A cewar shugaban kungiyar, tsohon gwamnan babban bankin kasa da El-Rufa’i sun dade suna magana kan cire tallafin a duk wani fage da suka samu kansu.

“Na daga cikin abin da zai faru bayan an janye tallafin iskar gas (desiel), farashin duk wani abu da za ka yi tunani ya tashi a matsayin litar dizal a yanzu ana sayar da shi a kan N850,” in ji Shugaban na IPMAN.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button