Labaran Duniya

Toffa Rikici Yaci Gabada Ballewa Tsakanin Jan’iyar PDP Da APC Yanzu A…

Har zuwa yanxu ananan ana ci gaba da cacar baki tsakanin kusoshin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, da kuma na jam’iyyar hamayya ta PDP, kan wasu zarge-zargen hare-hare da bangarorin biyu ke yi wa junan su.

Jam’iyyar APC mai mulki dai na zargin wasu ‘yan jam’iyyar PDP da kai wa magoya bayan jam’iyyar hari, in da suka kashe mutum guda 1 da kuma raunata wasu fiye da mutum goma.

Jam’iyyar ta APC, ta ce an kai wa magoya bayan nata da ke share-share a Gusau, babban  birnin jihar ta zamfara hari ne.

Malam Yusuf Idris Gusau, shi ne sakataren watsa labarai na jam’iyyar APC a jihar, ya shaida wa BBC cewa, Matasan wanda magoya bayan jam’iyyarmu ne na aiki a GRA, sai kawai ga magoya bayan jam’iyyar PDP, nan take suka kaddamar musu hari da bindigu.

Ya kara da cewa, Batun ace magoya bayan namu ne suka takali fada sam ba gaskiya bane, domin da hakan ne da suma an gansu da bindigar har ma su yi harbi suma.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button