Football News

Ranar Lahadi ne kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain ta yi nasara a kan Olympic Marseille…

A ranar Lahadi ne kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain ta yi nasara a kan Olympic Marseille da ci 1-0 a wasan mako na 11 a babbar gasar Ligue 1.

Dan wasa Neymar ne ya ci kwallon da ya bai wa kungiyar ta PSG maki ukun da take bukata a karawar da suka yi a wasan hamayya a Parc des Princes .

Dan wasan Brazil, ya ci kwallon a minti na 45 kuma na 200 a lik tun daga Santos da kuma Barcelona da kuma Paris St-Germain.

PARIS

Dan wasa Lionel Messi ya buga wasan ya kuma samu dama biyu ta cin kwallo, sai dai mai tsaron raga Pau Lopez ya nuna kwazonsa yayin da ya hada Lionel messi cin kwallo ko daya

Marseille ta karasa gumurzun da ‘yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bawa Samuel Gigot jan kati, sakamakon ketar da ya yi wa dan wasan PSG wato Neymar.

Marseille ta samu damar cin kwallo ta hannun Jonathan Clauss, amma Gianluigi Donnarumma ya tsare ragar tasa yadda ya kamata.

Da wannan sakamakon ne PSG, wadda ta ci wasa tara da canjaras biyu a karawa guda 11 ta ci gaba da jan ragamar teburin Ligue 1 da tazarar maki uku tsakaninta da Lorient ta biyu.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button