Football News

Karim Benzema Ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Kwallon kafa Na Duniya…

A Ranar Litinin ne Karim Benzema dan kwallon tawagar Faransa ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya da ake kira Ballon d’Or na shekarar 2021/22.

Dan wasan na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid shi ne na baya-bayan nan da ya lashe kyautar daga kungiyar Santiago Bernabeu a bikin da French Football aka gudanar.

Wannan Kyautar ita ce ta 66 da aka yi bikin karrama ‘yan wasan tamaula da suka yi fice a duniya da aka yi a kasar Faransa.

Dan wasa Benzema ya zama na 10 da ya lashe Ballon d’Or daga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, bayan da Luka Modric ya dauka a 2018 daga kungiyar.

Dan wasa Alfredo Di Stéfano shi ne na farko da ya fara lashe kyautar daga Real Madrid a shekarar 1957, sannan ya kara zama zakara a shekarar 1959. 

Dan wasa Raymond Kopa, wanda ya taka leda tare da Di Stéfano, shi ne ya lashe kyautar Shel 1958 na biyu daga Real Madrid, sannan Stefanano da ya dauka karo na biyu a shekarar 1959.

Sauran ‘yan wasan da suka lashe Ballon d’Or a Real Madrid kuma sun hada da Zinedine Zidane a 1998, wanda ya karba daga hannun Ronaldo Nazario na Inter Milan, wanda ya lashe a 1997 da kuma a 2002, wanda ya zama zakara a Real Madrid. Figo ya dauki Ballon d’Or a Real a 2000, sai Michael Owen a 2001 da Cannavaro a 2006 da kuma a 2007.

Shi kuwa dan wasa Cristiano Ronaldo Ballon d’Or biyar ya dauka a tarihin tamaularsa guda hudu a Real Madrid da kuma daya a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a 2008

Kyaftin din tawagar Portugal wanda ke wasa a Old Trafford yanzu haka shima ya lashe a shekarar 2013 da 2014 da 2016 da kuma 2017.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button