Labaran Hausa

Hukumar Karota Tana Neman Wani Dan Adai dai ta Sahu daya Dauko Kura Tayi Kokarin G…

Hukumar kula da sufurin motoci da babura a jihar Kano dake arewacin Nigeria (KAROTA) ta ce tana ci gaba da neman wani mai tukin baburin a-daidaita-sahu ruwa a jallo bayan da ya dauko wata kura da ta yi yinkurin tserewa a tsakiyar kasuwa.

Hukumar ta KAROTA ta ce jami’anta suna nan neman mai tukin baburin a-daidaita-sahun saboda abin da ya yi ya saba da doka, don kuwa bai kamata ya dauko dabbar daji a cikin babur ba.

Mai magana da yawun hukumar ta KAROTA, Nabulisi Abubakar ya shaida wa BBC cewa ita kura dabbar daji ce ba tunkiya ko akuya ba ce, dabba ce mai hatsari da bai kamata a bar ta tana gararamba a cikin mutane ba batare da tsaro ba.

Yakara da cewa “Muna nan muna ci gaba da neman wannan matukin baburin a-daidaita-sahun a yanzu haka, kuma yanzu haka muna da lambobin babura guda biyu da muke zargi, matukar kuma muka kama direban, to kotu za mu kai shi kai tsaye ba tare da wani bata lokaci ba.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button