World News

Gwannatin Shugaban Kasar Nigeria Muhammadu Buhari Tayi Alfahari da Aikin Datayi a Mulkin ta…

Shugaban kasar Nigeria General Muhammadu Buhari ya bayyanawa duniya cewa gwamnatinsa ta share wa yan Nigeria hawayensu bisa manya-manyan aiyukan ci gaba da ta gudanar a mulkinnansa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a yayin bude taron bibiyar kwazon ayyuka na ministoci domin yin duba a kan cimma nasarar aiwatar da kudirori 9 na gwamnatin tasa.

A cikin jawabin bude taron, Shugaba Buhari ya lissafa irin gagaruman nasarorin da ya samu a bangaren harkokin noma, da tattalin arziki, da gine-gine , da tsaro, dakuma harkar lafiya, sannan kuma yaki da cin hanci da rashawa da dai sauransu.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya shaida hakan ne ga wadanda su ka halarci taron, da su ka hada da tsohon shugaban kasar Kenya da ya bar mulki kwanan nan, Uhuru Kenyatta.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button