World News

Farfesa Emmanuel Osodoke, ya ce mambobin kungiyar tasu za su fuskanci wahala wajen komawa jami’o’insu

Shugaban kungiyar malaman Jami’o’i a Najeriya, Farfesa Emmanuel Osodoke, ya ce mambobin kungiyar tasu za su fuskanci wahala wajen komawa jami’o’insu a ranar Litinin saboda basu da kudin da zasu hau mota.

Shugaban na hukumar ta ASUU ya bayyana haka ne a jiya Lahadi, yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels dangane da janye yajin aikin na hukumar ta ASUU a ckin wani shiri da gidan talabijin din sukeyi mai suna Sunday Politics.

Shugaban hukumar Farfesa Osodoke ya ce a lokutan baya malaman Jami’a na zama a gidajen da aka tanada musu kusa da makaranta, amma a yanzu ba haka lamarin ya kasance ba domin suna zaune ne nesa da Jami’oin da suke koyarwa saboda yawancinsu basa samar musu wuraren zama.

“A lokutan baya, malami zai iya taka wa da kafa yaje makaranta saboda suna zaune a cikin gidaje da aka tanadar musu, amma a yanzu lamarin ya sauya, inda suke tafiyan kilomitoci 20 zuwa 30 kafin isa makaranta. Ta ya ya za su iya biyan kudin mota zuwa aiki,” in ji shugaban nasu wato Osodoke.

Ya ce za su fuskanci wahalhalu da dama wajen biyan kudin motar komawa aiki domin koyar da dalibai saboda ba a biya su ba har na tsawon watanni takwas.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button