Football News

Dan Wasan Kwallon Kafa Na Portugal Diagi jota Bazai Sami Damar Buga Wasan…

Dan wasan tawagar Portugal, mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Diago Jota, ba zai sami damar buga gasar kofin duniya ba, sakamakon wani raunin da ya ji in ji Jurgen Klopp.

Dan wasa mai shekaru 25 ya ji ciwo a wasan Premier League ranar Lahadi da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta ci kungiyar kwallon kafa ta Manchester City da ci 1-0 a Anfield.

Klopp ya ce ” Dan wasa Jota zai yi jinya mai tsawo, muna magana kan cewa zata kasance jinyace ta watanni da dama shiyasa bazai sami damar buga gasar kofin duniya ba.”

Jota ya rubuta a kafarsa ta sada zumunta ”Bayan daren murna a Anfield tawa ta kare a mummunan yanayi, kuma daya daga cikin mafarkai na ya rushe gabaki dayan sa.”

Dan kwallon bai fara buga gasar Premier a bana ba, sakamakon jinya, wanda ya koma taka leda ranar uku ga watan Satumba a wasan da Liverpool ta tashi 0-0 da kungiyar kwallon kafa ta Everton.

A cikin watan dan wasan ya buga wa Portugal wasan da ta doke Jamhuriyar Czech da ci 4-0, ya kuma ci kwallo daya daga ciki.

A ranar 20 ga watan Nuwamban shekarar 2022 za a fara gasar cin kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button