Labaran Duniya

Asiwaju Bola Ahmad Tunubu Yayi Alkawarin Shawo Kan Matsalar Dake Damun Nigeria Yanzu a…

Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin shawo kan matsalolin da ke arewacin Najeriya ke fuskanta da kuma kasar baki daya muddin ya sami nasarar zama shugaban kasa.

Dan takarar Bola Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wata magana a wani taro da kungiyoyi masu fada aji na arewacin Najeriya suka hada da kungiyar dattawan arewa da kuma Arewa Consultative Forum suka shiryawa ‘yan takarar shugabancin kasa a Arewa House dake a JIhar Kaduna.

Tinubu ya kara da cewa cikin abubuwan da zai fara yi shine kammala aikin wutar Mambilla da aka shafe tsawon shekaru ba tare da yin aikin ba, inda ya ce tashar za ta samar wa da kasar wuta mai karfin wadda takai kimanin megawatt 3,050 da kuma zai kasance daya daga cikin tasha mafi girma a fadin kasar baki daya.

“Abin da ya kawo jinkirin kammala wannan aikin shine rashin isassun kudade a kasar. Ba ma kebe isassun kudade ga manyan ayyuka masu daukar dogon lokaci. Za mu kammala wadannan aiki saboda muna zuwa da wani tsari mai kyau ga kasar ta Nigeria,” in ji Tinubun.

Tinubun ya kuma ce zai kawo masu zuba jari a ciki da kuma wajen kasar wadanda za su kammala aikin da kuma zai kawo wa kasar ci gaba cikin gaggawa.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button