Innalillahi Wainna Ilaihi RajiUn: Yadda Matasa Suka Fito Zanga Zanga Bayan Kashe wa…

Wasu matasa a jihar Bauchi sun fito zanga-zanga a yau dinnan tare da toshe babbar hanyar zuwa jihar Bauchin bayan kisan wani mutum mai shekaru 67 mai suna Adamu Babanta da ke zaune a yankin Yelwa Labura a jihar bauchin.
Tun da sanyin safiya ne da misalin karfe 7, matasan suka yi dirar mikiya a kan babban titin jihar Bauchi -Tafawa Balewa a gaban kwalejin aikin gona, inda kuma suka toshe hanyar tare da kawo cikas wajen wucewar ababen hawa ta hanyar, wanda hakan ya sanya da yawa komawa amfani da wata hanyar ta daban.
Jaridar Nigeria Tribune ta ruwaito cewa makwabcin mutumin ne mai suna Mohammed Damina Galadiman Dass yayi awon gaba da shi da motarsa wanda kuma ya kai ga mutuwarsa.
Wani dan uwan mamacin wanda ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce ana zargin wanda ya kashe dan uwannasa da yunkurin yin lalata da wata budurwa mai shekaru 18 mai suna Khadija wadda kuma ta kasance ‘ya ce ga marigayin.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ne amma rundunar ta ce an shawo kan matasan da suka fito zanga-zanga tare da girke jami’an tsaro domin samar da zama lafiya a yankin baki daya.
Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.