Football News

Za’a Bayyana Gwarzon dan Kwallon Kada Duniya Yanzu a…

Za a bayyana gwarzon dan kwallon duniya wanda za a bai wa kyautar Ballon d’Or a ranar Litinin 17 ga watan Oktoba na kakar.

Mujallar Frence Football ce ke karrama dan wasan tamaula da ya taka rawar gani da ya kasance ba kamarsa a gaba daya fadin duniya.

Wannan dai shi ne karo na 66 da za a gudanar da bikin bada kyautar wanda za a yi a Faransa, don fayyace gwarzon dan kwallon kafa na kakar shekarar 2021/22.

Tun a ranar 12 ga watan Agustan shekarar 2022 aka bayyana wadanda yake takara.

A karo na farko a tarihin Ballon d’Or za a bayyana gwarzo bisa kwazonsa a kakar tamaula ne, maimakon shekara daya.

Dan wasa Lionel Messi mai rike da kyautar bara baya daga cikin ‘yan takara, kuma a karon farko a shekara 17 da ba sunan kyaftin din Argentina.

Tun daga shekarar 2008 Messi da Cristiano Ronaldo ke bani in baka wajen lashe kyautar ta ballon d’Or, in banda a shekarar 2018 da Luka Modric ya zama zakara a wannan karon.

To sai dai kuma a wannan karon masana na ganin ba wanda ya kamata ya lashe kyautar fiye da dan kwallon tawagar Faransa da kuma kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, wato dan wasaKarim Benzema.

Dan wasan shi ne ya dauki La Liga a bara da kuma Champions League, kuma shi ne yakasance kan gaba a cin kwallaye a babbar gasar tamaula ta Sifaniya da ta zakarun nahiyar Turai.

Maza da ke takarar Ballon d’Or:

1) Thibaut Courtois (Real Madrid)

2) Rafael Leao (AC Milan)

3) Christopher Nkunku (RB Leipzig)

4) Karim Benzema (Real Madrid)

5) Riyad Mahrez (Manchester City)

6) Casemiro (Real Madrid)

7) Heung-Min Son (Tottenham)

8) Fabinho (Liverpool)

9) Kylian Mbappe (Paris Saint-Germain)

10) Mohamed Salah (Liverpool)

11) Joshua Kimmich (Bayern Munich)

12) Trent Alexander-Arnold (Liverpool)

13) Vinicius Junior (Real Madrid)

14) Bernardo Silva (Manchester City)

15) Luis Diaz (Liverpool)

16) Robert Lewandowski (Barcelona)

17) Mike Maignan (AC Milan)

18) Harry Kane (Tottenham Hotspur)

19) Darwin Nunez (Liverpool)

20) Phil Foden (Manchester City)

21) Sadio Mane (Bayern Munich)

22) Sebastien Haller (Borussia Dortmund)

23) Luka Modric (Real Madrid)

24) Antonio Rudiger (Real Madrid)

25) Cristiano Ronaldo (Manchester United)

26) Kevin De Bruyne (Manchester City)

27) Erling Haaland (Manchester City)

28) Virgil van Dijk (Liverpool)

29) Dusan Vlahovic (Juventus)

30) Joao Cancelo (Manchester City)

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button