Labaran Hausa

DaDumiDuminSa: Darikar Tijjaniya Tanada Alamajirai 3,000,000,000 Kuma Aljanu Ne….

Toffa Babbar Magana Yanzu Babban Malami Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce Aljanu biliyan uku su ka karbi Darikar Tijjaniya.

Babban Malamin ya ce daga cikin wadannan Aljanu, akwai mukaddamai miliyan dari biyu Akwai yiwuwar a rika amfani da Aljanun domin maganin masu garkuwa da mutane.

Shehin malamin ya bayyana cewa akwai wasu kebantattun mutane da su ke iya sadu wa da aljanu. Ya ce ya na daga cikin masu mu’amala da su.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce wasu suna ganinsu, har su yi magana da su, kamar yadda shaidanun mutane su ke hulda da shaidanun Aljanu.

A cewar Sheikh Dahiru Usman Bauchi akwai Aljanu muminai, daga cikin su har mabiya Darikar Tijjaniya wanda yanzu adadinsu ya zarce biliyan uku.

Wannan Kenan Kadan Daga Abunda Malama Dahiru Usman Bauchi Ya Bayyana Kenan.

Mun Gode Sosai Da Sosai Masoya Bisa Ziyarar Ku a Wannan Gida Mai Albarka Na Musamman Gidan Labarai Masu Inganci Na’ Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button