Kannywood
Innalillahi Wainna Ilaihi Raji’Un: Allah Yayiwa Mahaifiyar Jarumin Kannywood Tijjani Faraga, Rasuwa Yanzu….

Qalu Innalillahi Wainna Ilaihi Raji’Un Allah Yayiwa Mahaifiyar Jarumin Kannywood Malam Tijjani Faraga Rasuwa Allah Yajikan Musulma.
Jarumi a Kannywood, Malam Tijjani Faraga, ya bayyana irin halin kaɗuwa da ya shiga saboda rashin mahaifiyar sa da ya yi, wato Hajiya Rabi’atu Usman.
Da ya ke tattaunawa da mujallar Fim kwana uku bayan rasuwar mahaifiyar tasa, Malam Tijjani ya ce: “Gaskiya ban taɓa rashin wani ɗan’adam da ya kai mahaifiya ta ba. Tun lokacin da ta rasu a rikice na ke.

Innalillahi Wainna Ilaihi Raji’Un Marigayiyar dai ita ce babbar yaya ga Babban Limamin garin Jos, Sheikh Lawal Adam. Allah Yaji Kanta da rahama idan tamu tazo yasa mu cika da kyau da iman ameen Summa Ameen.