Kannywood

Masha Allah; Yanzu An Sako Ragowar Fasinjojin da Yan Bindiga Suka Kama a…

Gidan labarai na Edunoz ya tabbatar da cewa an sako dukkan fasinjojin da suka rage a hannun yan ta’adda bayan da aka sace su a watan Maris na wannan shekarar cikin wani babban jirgin kasan da ke kan hanyar sa ta zuwa Kaduna daga garin Abuja.

Gwamnatin Najeriya ce ta sanar da wannan labarin ne cikin wata sanarwa da Farfesa Usman Yusuf, sakataren wani kwamitin ma’aikatar tsaron Najeriya mai suna CDSAC a ranar Laraba.

“Ina mai farin cikin sanar da kasa da ma duniya baki daya cewa da yammacin yau Laraba 5 ga watan Oktoba 2022, kwamitin mutum bakwai da hafsan hafsoshin dakarun tsaron kasa Janar L. E. O. Irabor ya sami nasarar ceto mutane 23 da suka rage a hannun ‘yan ta’adda bayan da suka kai hari kan jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris na 2022.

Yakara da cewa “Wannan kasar na cike da godiya ga sojojin Najeriya a karkashin jagorancin hafsan hafsoshin sojojin kasar, wanda shi ne ya jagoranci aikin daga farkonsa har zuwa karshe. Haka ma, sauran hukumomin tsaro da suka taimaka wajen nasarar da muka samu a wannan aikin.”

Sai dai har kawo yanzu babu rahotannin inda aka kai fasinjojin da aka sako, ko kuma yadda aka iya karbo su daga hannun ‘yan Boko Haram din da suka yi garkuwa da su.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button