Kungiyar Kwallon kafata Manchester City Tayiwa….

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta doke kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da ci 6-3 a wasan makon na takwas a babbar gasar Premier League da suka kara ranar Lahadi a Etihad.
Tun kafin hutu kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta ci kwallo 4-0 ta hannun Phil Foden da Erling Haaland kowanne ya ci bibiyu.
Bayan da suka huta suka koma karawar zagaye na biyu bayan hutu Foden da Haaland kowanne ya kara zura kwallo a raga.
Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta zare uku ta hannun Dos Santos, sannan Anthony Martial ya zura biyu a raga daya daga ciki kuma a bugun fenariti.
Da wannan sakamakon Manchester City tana mataki na biyu a kan teburin Premier da maki 20, United kuwa tana nan da makinta 12 tana ta shida a teburin wasannin bana.
Kungiyar Manchester City ta yi nasara karo uku a jere a kan United tun bayan doke ta hudu da ta yi tsakanin watan Afirilun 2013 zuwa Nuwambar shekarar 2014.
Manchester United ta yi rashin nasara karo na 18 a Premier League a hannun City, – Liverpool da Chelsea sun yi nasara a kan United irin haka a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.