Labaran Hausa

Tsohon Shugaban Kasar Nigeria Obasanjo Yace Babu Wani Dan Takara daya Marawa Baya….

Tsohon Shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce babu wani ɗan takarar shugabancin ƙasa da yake mara wa baya a babban zaɓen ƙasar daza’a gudanar na shekarar 2023 da ke tafe, a cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Da yake magana a Minna, babban birnin Jihar Neja yayin ziyarar da ya kai wa Tsohon Shugaban Mulkin Soja Badamasi Babangida ranar Lahadi, Obasanjo ya ce Najeriya ce a gabansa ba wani ɗan takara ba.

“Ba ni da ɗan takara, ƙasa ce a gabana,” in ji shi. “Na zo ziyarar ɗan uwana da ya yi ‘yar rashin lafiya da yayi fama da ita, wanda na so na yi hakan tun yana Landan amma sai ya koma gida a ranar da na isa Landan ɗin.”

A makon da ya gabata, an ga Obasanjo a birnin Landan na ganawa da ɗan takarar jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, da sauran ‘yan siyasa. Kafin haka, ɗan takarar APC, Bola Tinubu, ya ziyarce shi a birnin Abeokuta na Jihar Ogun.

Bisa al’ada, akasarin masu neman shugabancin kasar Najeriya kan kai wa tsofaffin shugabannin ziyara don neman goyon bayansu a kowace shekarar zaɓe.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button