Labaran Hausa

A wani Bin’cike da Akai An Gano Yan Nigeria Sun Sha Guys Ta Sama da Naira Biliyan 599.11 Yanzu….

A wani bincike da aka gabatar an gano cewa iya Yan kasar Najeriyar sun sha giyar da takai kimanin kudi har naira biliyan 599.11 a cikin wata shida daga watan Janairu zuwa watan Yunin shekarar 2022, a cewar bayanan manyan kamfanoni sarrafa giya guda huɗu da ke Najeriya.

Bayanan da kamfanonin suka fitar da suka hada da Guinness da Champion na cewa sun samu habbakar kuɗaɗen shiga a waɗannan watanni shida da watan janairu zuwa watan Yunin shekararnan.

Kuɗaɗen shigar kanfanunuwan ya karu ne da kashi 31.2 cikin 100 idan aka kwatanta da naira biliyan 456.44 da suka samu a shekara da ta wuce ta 2021.

Waɗannan alkaluma na nuna yadda ake samun ‘yan kasar Najeriya da ke rubanya adadin barasa da suke sha a wuni guda, a cewar rahoton.

Wannan bincike ya a zama barazana ga yan kasar Nigeria sakamakon karuwar adadin shan barasar yayi, mutane da dama sun shiga firgici musamman yan arewacin kasar saboda tunanin rayuwar yara masu tasowa.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button