Football News

Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea Ta Cinye Yar’jejeniya Datayi da dan Wasan faransa…

kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta cimma yarjejeniya da dan wasan baya na Faransa mai shekara 21, Wesley Fofana game da tafiyarsa kungiyar, sai dai sau biyu kungiyar da yake yi ma wasa, wato Leicester City na kin amincewa da tayin da Chelsea din ta yi. Inda Leicester ke bukatar Blues din su biya sama da £80m kan dan wasan.

Haka kuma da alama dan wasan tsakiya na Netherlands, Frenkie de Jong, da dan wasan gaba na Gabon, Pierre-Emerick Aubameyang, na kan hanyarsu ta komawa Stamford Bridge da wasa, kasancewar Chelsea din ita ce kan gaba a kokarin daukar ‘yan wasan daga Barcelona.

Sai dai kuma, De Jong ya fada wa abokan wasansa na Barcelona cewar da yiwuwar ya koma kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.

Amma ita Barcelona a shirye take ta fara tattaunawa da Chelsea kan Aubameyang.

kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta tattauna da kungiyar Atletico Madrid kan yiwuwar dauko dan wasan gaba na Sifaniya, Alvaro Morata, mai shekara 29, a kan kudi £30m. (The Athletic, via Mail Online)

Haka nan kuma Manchester United din ta kara jaddada wa Paris St-Germain cewar Marcus Rashford, ba na sayarwa ba ne.

Muna Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button