World News

Ƙungiyar kwadago ta NLC a Najeriya ta nemi gwamnatin Tarayya da ta kara albashin ma’aikata da kashi 50 cikin 100 lura da yanayin tsadar rayuwa

Ƙungiyar kwadago ta NLC a Najeriya ta nemi gwamnatin Tarayya da ta kara albashin ma’aikata da kashi 50 cikin 100 lura da yanayin tsadar rayuwa da ake ciki a Nigeria.

Kungiyar ta NLC ta mika wannan bukata ne ga shugaba Muhammadu Buhari ta wasikar da ke dauke da sa hannun shugaban kungiyar Ayuba Wabba.

Wasikar ta yi tuni da cewa gwamnonin su suka karfafa batun janye tallafin mai, da kawo batun ritayan ma’aikatan gwamnati a shekara 50, da kuma rage kudaden da ake bai wa majaliasa domin aikin mazabu.

Ƙungiyar ta yi suka ga gwamnoni kan wadannan shawarwari, su na mai cewa duk wanda ya goyi bayan ra’ayinsu to ba shi da maraba da makiyin gwamnati.

kungiyar ta NLC ta ce batun karin albashi ne abin da ya kamata a mayar da hankali a kai, domin a wannan lokaci shi ne abu mafi muhimmanci dayakamata gwamnati tayi

Masu fafutikar dai na ganin akwai bukatar gwamnati take amfani da yanayin kasa da abubuwan da ke faruwa wajen fayyace albashi da samawa ‘yan kasar sauki.

Munu Matukar Godiya Zuwa Gare’ku Godiya Mai Tarun Yawan Gaske Masoya Kuci Gaba’da Kasan’Cewa da’mu a Wannan Gida Mai Albarka Na” Edunoz.Com.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button