Labaran Hausa

Hukumar Kwastam ta Samu Nasarar Kama Kwantena Cike da Kwayar Aji Garau…

Dakarun hukumar kwastam ta Najeriya ta yi nasarar kama wata kwantena a cike da haramtacciyar ƙwayar a-ji-garau ta tramadol a tashar Apapa ta Jihar Legas mai darajar fiye da naira biliyan ɗaya.

A wani rahoton da hukumar ta wallafa a shafinta na sada zumunta ranar Juma’a ya ce masu kwantenar sun bayyana kayan ciki a matsayin tukunyoyi na girki, kuma suka biya biliyan 1.3 a matsayin kuɗin kayan.

Sai dai da jami’an kwastam suka buɗe kayan sai suka tarar da katan-katan na tramadol ƙunshe a cikin tukunyoyin guda 273.

“A cikin kowane katan na ƙwayar na ƙunshe da kwali 50, kowane kwali na ƙunshe da fakiti 10, kowane fakiti na da ƙwaya 10,” a cewar Kwantirolan Kwastam na Apapa wato Malanta Yusuf.

Hukumar ta Kwastam ta ce ta ƙwace kayan kuma yanzu haka ta miƙa su ga hukumar NDLEA mai yaƙi da ta’ammali da miyagiun ƙwayoyi a Najeriya.

Muna Godiya Ta Musamman Da Ziyartar Wannan Gida Mai Albarka Na Musamman “Shafin Labarai na Edunoz.Com”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button