Kannywood

Majalissar Dattawan Nigeria Ta Baiwa Hafsoshin Tsoro wa’adin Wata Hudu….

Majalisar Dattawan Najeriya ta bai wa manyan hafsoshin tsaron kasar wa’adin na wata hudu domi su kawo karshen matsalolin tsaron da ke addabar sassan kasar.

Wannan na zuwa ne bayan da majalisar ta yi wata doguwar ganawa da shuwagabannin a jiya, duk da cewa majalisar tana a hutu.

A baya-bayan nan dai lamarin tsaro ya sukurkuce, al’amarin da ya kai ga wasu ‘yan majalisar yunkurin tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari muddin bai sauya salon tsaron ba.

Majalisar dokoki ta bayyana damuwarta game da ƙaruwar rashin tsaro a ƙasar ta Nigeria, musamman harin da ƴan ta’adda suka kai kwanan nan a Abuja.

Shugaban majaliar dattijai, Ahmad Lawan, ya kira shuwagabannin tsaro domin taron gaggawa a jiya, inda ya lamari ne mai ban tsoro.

A taron, sanatoci sun bai wa shugabannin tsaro shawarwarinsu a kan yadda za a kare Birnin Tarayya dama ƙasar gaba daya.

Mafi yawan kwamitocin majalisar dokokin su ma sun gana da shugabannin tsaro akan matsalolin tsaron a Juma’ar da ta wuce don sanin me ake ciki a ƙasar ta Nigeria.

Majalisar wakilai ta ce ƴan ta’adda suna barazanar kai hari Abuja inda fadar shugaban ƙasar take, inda suka ce dole hukumomin tsaro su yi maganin masu tayar da ƙayar bayan.

A cikin makonnin da suka wuce, birnin tarayya ya fuskanci barazana daga wurin ƴan tada keyar baya akan kai hari kan wasu dakarun sojji da gidan yarin Kuje dake garin Abuja.

BBC HAUSA

A ranar Alhamis ɗin da ta wuce ma, ƴan ta’adda sun kai wa sojojin da ke shingen bincike na Dutsen Zuma mai nisan kilomita kadan daga cikin birnin na Abuja.

Muna Godiya Ta Musamman Da Ziyartar Wannan Gida Mai Albarka Na Musamman “Shafin Labarai na Edunoz.Com”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button