Ana Zargin Yan Vijelante da Kashe Wani Malamin Makaran’tar Allo…

Ana zargin ‘yan kungiyar yan sintiri ta (vigilante) da kashe wani malamin makarantar allo a unguwar Dabai, da ke a karamar hukumar Gwale a garin Kano.
Shi dai malamin mai suna Musa Mai-Almajirai, sanannen malamin Qur’ani ne a unguwar ta danai, inda yake da daruruwan almajirai dake basu ilimin addini.
Ana zargin ‘yan kungiyar Vigilante da yi wa malamin dukan tsiya a wani ofishinsu bayan da aka kai shi can bisa zargin da wata mata ta yi masa na yunkurin satar yaro.
Jaridar Premium Times ta intanet ta ruwaito cewa dan malamin, Ibrahim ya sheda mata cewa, ”Mahaifin nasa yana tafiya ne sai ya ji kukan jariri sabuwar haihuwa a wata bola kusa dashi.
Sai ya je ya dauki yaron domin tausayawa kawai sai wata mata ta soma yi masa ihu, tana ce masa barawon yara.”
”Kururuwar da matar ta yi ce ta janyo ‘yan kungiyar sintirin da sauran jama’ar unguwar wadanda suka rufe shi da duka,” a cewar dan nasa.
Dan malamin Ya kara da cewa, ”Daga nan sai yan sintirin suka tafi da shi ofishinsu suka ci gaba da dukansa. Har saida ya fadi sumamme.”
Dan malamin ya ce,” Bayan da wasu ‘yan unguwar suka gane shi sai suka garzaya da shi asibiti, inda rai yayi halinsa a hanya.”
Dan malamin ya sheda wa jaridar cewa yanzu haka ‘yan-sanda sun kama shugaban ‘yan-sintirin na unguwar, mai suna Munkaila, inda ake bincikensa a caji ofis na Rijiyar Zaki.
Muna Godiya Ta Musamman Da Ziyartar Wannan Gida Mai Albarka Na Musamman “Shafin Labarai na Edunoz.Com”.