Kannywood

Toffa Gwabnatin Nigeria Ta Kashe Manyan Kudade Akan Har’kar Man Fetur a

Gwamnatin Najeriya ta kashe kudi har naira tiriliyan biyu wajen biyan kuɗin tallafin man fetur cikin wata shida na shekarar 2022, a cewar rahoton babbab kamfanin mai na ƙasar wato NNPC.

Kamfanin dillancin labarai na Edunoz ya ruwaito cewa a ranar Talata ne kamfanin NNPC ya gabatar da rahoton ga kwamatin asusun kasafi na ƙasa wato Federation Accounts Allocation Committee (FAAC).

Saboda ƙarin yawan kuɗin da ake biya na tallafin ya sa NNPC yaki bai wa gwamnatin ƙasar ko kwandala ba a matsayin riba cikin shekarar nan, a cewar rahoton.

A shekarar 2021, gwamnati na biyan naira biliyan 100 ne duk wata a matsayin kuɗin tallafi. Shugabannin kamfanin ba su ce komai ba lokacin da Edunoz ya nemi ƙarin bayani.

A watan Janairu ne ya kamata ƙasar ta dakatar da biyan tallafi amma sai gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ɗage matakin, tana mai cewa nauyin zai yi wa ‘yan ƙasa yawa yayin da ake fama da hauhawar farashi.

Najeriya na shigar da dukkan man fetur ɗin da ake amfani da shi a ƙasar saboda matatun mai da ke cikin gida ba sa aiki.

Muna Godiya Ta Musamman Da Ziyartar Wannan Gida Mai Albarka Na Musamman “Shafin Labarai na Edunoz.Com”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button