Kannywood

Kasar Ghana Tana Zaman Kota Kwana Saboda Wata Cuta Mai Suna Marburg

Hukumar da take ke yaki da cutuka masu saurin yaduwa a kasar Najeriya, ta kasance tana cikin shirin ko-ta-kwana, bayan da aka samu bullar cutar Marburg a kasar Ghana.

A wata sanarwa da hukumar ta NCDC ta fitar ta na cewa Najeriya ta tanadi duk wasu abubuwa na gwaje-gwajen gano cutar da kuma yadda za su magance ta idan ta bulla a kasar ta Nigeria

Bayan haka hukumar ta kara da cewa likitocin kasar nan sun shirya wa cutar ta Marburg mai alaka da cutar Ebola, an kuma tsaurara duk wasumatakai na sa-ido kan cutar ta Marburg

Har zuwa yanzu dai ba a samu rahoton bullowar cutar a kasar Nigeria ba, wacce itace kasar da ta fi kowacce kasa yawan al’umma a gaba daya nahiyar Afirka.

Tun a farkon makon nan ne dai,hukumomin lafiya na kasar Ghana suka tabbatar wa duniya bullar wannan cuta a kasar ta Ghana inda aka gano wasu mutum biyu da aka tabbatar da suna dauke da wannan cuta har takai da cewa rai yayi halinsa.

sannan kasar ta kuma killace gomman mutane, wadanda ake tunanin suma suna dauke da wannan cuta ta Marburg
kasar ta Ghana tayi hakane domin dakatar da cutar kafin tayi yaduwar da zatafi karfinsu.

https://l.facebook.com/l.php?u=https%3A%2F%2Fbbc.in%2F3RL4rOh&h=AT2s7_CsAgchq3GSL18N5Tnd_TgLluXxN1ztFeZaL2_UMjsdnBhecBgPQZmSh6dPJ7MzuQY_FN5A4DR_qYWLuPzhsGVU8QVze1Vhya4sCiWMMo5gXbFS5Ixv7Z_v-84GvnAB6RJQNg

Muna Godiya Sosai da Sosai Masoya Bisa Ziyarar Wannan Gida Mai Albarka Na Musamman Gidan Labarai Na” Edunoz.Com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button